BBC navigation

Bunkasar tattalin arzikin China mai ban-mamaki

An sabunta: 2 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:32 GMT

Tun a shekarar 1978 aka dasa tushen bunkasar da tattalin arzikin China ke yi daga shekarun 1990s lokacin da Jam'iyyar Kwaminis ta fara kawo sauye-sauyen jari-hujja, musamman a bangaren aikin gona.

Habakar tattalin arzikin China cikin hanzari

Habakar tattalin arziki ta fadada ne cikin hanzari a shekarun 1990 sakamakon sayar da kamfanonin gwamnati, da kuma bude kofa ga masu zuba jari daga kasashen waje. Kamfanonin kasashen waje ba su yi nawa ba wajen gina masana'antu a China don su ci gajiyar rashin tsadar biyan ma'aikata.

Karuwar amfani da makamashi a China da tasirin hakan a kan muhalli

Makamashin da China ke samarwa da kuma tasirinsa a kan muhalli

Karuwar yawan makamashin da China ke amfani da shi manuni ne na irin habakar tattalin arzikinta. Kasar ta gina dubban tashoshin samar da wutar lantarki don bayar da wutar ga dukkanin sababbin masana'antu da ma jama'ar da ke karuwa a birane.

Sai dai kuma hakan ya yi tsiri matuka gaya a kan muhalli, tunda gurabatar yanayi ta karu, musamman ma daga tashoshin samar da wutar lantarki masu dimbin yawa da ke amfani da ma'adanin kwal. Tasirin wannan ci gaba a kan muhalli a bisa ma'aunin tattalin arziki, kamar yadda aka nuna a taswira ta sama daga dama, ma'auni ne na kudaden da gurabatar yanayi ke lashewa da kuma yadda yake lakume albarkatun kasa masu karewa.

Karuwar jama'a a biranen China

Adadin karuwar jama'a a biranen China

Yayin da ake ta giggina masana'antu a China, miliyoyin mutane sun yi kaura daga yankunan karkara don neman aiki mai gwabi a birane. Hakan kuma ya samar da wata sabuwar kasuwa ga kayan tireda ta cikin gida, inda bukatar kayayyakin yau da kullum ta karu ta kuma kara ingiza habakar tattalin arzikin kasar da fadadar birane.

Karuwar wadata a China

Habakar tattalin arzikin China cinikin hanzari ta kara wa al'ummar kasar wadata. Ana iya ganin haka musamman a birane, inda albashin ma'aikatan masana'antu ya karu sosai, ya kuma kara yawan kudin kashewarsu--wato in aka debe haraji daga kudin shigar da suke samu. Ko da yake kudin da ake samu a yankunan karkara yana nan jiya-i-yau, kudaden kashewar mazauna yankunan na karkara sun karu daidai gwargwado.

Fadadar kasuwannin sayar da motoci

A kasashe masu tasowa a fadin duniya, mallakar mota alama ce ta cewa wuyan mutum ya fara kauri, kuma yayin da kudin shiga ke karuwa an samu karuwar mallakar motoci a kasar ta China.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.