BBC navigation

Ra'ayi Riga: Yakin neman zaben shugaban kasa a Amurka

An sabunta: 2 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:40 GMT

Garmaho

Ranar Talata mai zuwa ne dai za'a fafata zaben shugabancin kasar a Amurka tsakanin shugaba Barack Obama na jam'iyyar Democrat da kuma Mitt Romney na jam'iyyar Republican. To ko yaya kuke kallon yakin neman wannan zabe?

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

obama da romney

Shugaban Amurka, Barack Obama da mai kalubalantarsa Mitt Romney

Ranar Talata mai zuwa ne dai za'a fafata zaben shugabancin kasar a Amurka tsakanin shugaba Barack Obama na jam'iyyar Democrat da kuma Mitt Romney na jam'iyyar Republican.

To ko yaya kuke kallon yakin neman wannan zabe? Kuma wanne irin darasi ya kamata kasashen Afurka su koya daga zaben na Amurka?

Wasu kenan daga cikin batutuwan da zamu tattauna a filin Ra'ayi Riga.

Obama dai zai shiga wannan zabe ne tare da mataimakinsa, Joe Biden, yayin da Mitt Romney zai shiga zaben da Paul Ryan a matsayin mataimakinsa.

Sai dai kuma wannan zabe na zuwa ne a daidai lokacin da Amurkan ke fuskantar manyan kalubale da dama kama daga batun tattalin arziki zuwa batun dokar nan ta bada tallafin kiwon lafiya.

Sauran batutuwan dai sun hada ne da batun kwararowar baki cikin kasar da kuma batun manufofin Amurkan a huldarta da kasashen duniya.

Kasashen duniya dai sun sa ido sosai yayin da 'yan takarar biyu suka yi ta fafata a yakin neman zaben inda har aka yi ta muhawara akan batutuwa da dama.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.