BBC navigation

Sababbin shugabanni: Fatan al'ummar China

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 09:58 GMT

Sababbin shugabanni: Fatan al'ummar China

 • Jam'iyyar Kwaminis ta China na gab da aiwatar da sauyin shugabanci wanda ake yi duk shekra goma; ana kuma sa ran zai yi tasiri sosai a makomar kasar. BBC ta tambayi 'yan kasar ta China su tara su bayyana batu na farko da suke son sababbin shugabannin su tunkara.
 • Liu Zhixin
  Liu Zhixin wata uwa ce mai shekaru 25 a duniya daga Birnin Harbin a lardin Heilongjiang; tana da 'ya mai suna Liu Aitong. A cewarta: "Fata na shi ne makarantu za su sassauta matsin lamba a kan dalibai, su kuma karfafa musu gwiwa su karanta fannin da suke sha'awa don su zama abin da suke sha'awa a rayuwa. Yanzu haka dalibai na karatu ne kawai don su ci jarrabawa".
 • Wang Yi
  Wang Yi, dan shekara 27 daga Beijing; ba shi da aikin yi: "Ina ganin ya kamata sababbin shugabannin China su inganta yanayin siyasarmu ta yadda zai dace da sauran kasashen duniya, musamman ta hanyar tabbatar da dimokuradiyya da 'yancin 'yan jaridu. Ya kamata su kawo gagarumin sauyi a fagen siyasa. Hakn zai sanyawa matasa kyakkyawan fata da kwarin gwiwa a tsarin siyasa da tattalin arziki".
 • Xu Yong
  Xu Yong, dan shekara 19, ba shi da aikin yi, daga Birnin Handan, lardin Hebei: "Ina ganin rikicin Tsibirin Diaoyu ya zama matsala ce saboda yakin da China ta yi da Japan a tarihi. Ina kuma fata shugabanninmu za su kara kyautata wa talakawan China".
 • Tao Guangxue
  Tao Guangxue, mai shekaru 63; ma'aikacin gwamnati ne da ya yi ritaya kuma karamin mamba a Jam'iyyar Kwaminis, daga Birnin Harbin a lardin Heilongjiang: "A da ina kaunar Jam'iyya kuma na yi amanna da duk abin da take yi, amma abubuwa sun sauya saboda Jam'iyyar ba ta yi wani abin a-zo-a-gani ba a 'yan shekarun da suka gabata. Kamata ya yi a ce abin da gwamnati ta fi mayar da hankali a kai shi ne kyautata rayuwar jama'a. Za a dauki lokaci mai tsawo kafin mu samu mulkin dimokuradiyya da gwamnati mai tsage gaskiya. Ba yadda za a yi a maye gurbin Jam'iyyar, in ba haka ba sai kasar ta durkushe. Wannan Jam'iyyar ce kawai za ta iya mulkin kasar nan".
 • Yang Huijie da Qiao Yujiao
  Ma'aikatan otel Yang Huijie mai shekaru 28 daga Shangqiu, lardin Henan, da Qiao Yujiao mai shekaru 27 daga Chengde, lardin Hebei: "Muna aiki tukuru saboda mu samu karin albashi. Amma kuma muna bukatar shirye-shiryen gwamnati wadanda za su kare muradunmu, misali, inshorar lafiya ta ma'aikata".
 • Maerhaba
  Maerhaba, dalibin dokokin kasa-da-kasa, dan kabilar Uighur daga Yankin Xinjiang: "Ina ganin gwamnatin China tana taka rawar gani, amma ta wasu fuskokin ba abu ne mai sauki a yi adalci ko abin da ya kamata ba. Bisa la'akari da irin labaran da nake ji, ina ganin abin da ya kamata su fara tunkara cikin gaggawa shi ne rashin adalci da gazawar gwamnati".
 • Liu Hongmei
  Liu Hongmei mai shekara 25 daga Birnin Tianshui, lardin Gansu: "Abu mafi muhimmanci shi ne kiwon lafiya. Ba abin da za ka iya yi in ba ka da lafiya. Misali, ya kamata gwamnati ta aiwatar da wasu dokoki don tabbatar da lafiyar abinci".
 • Chen Jiazhen
  Chen Jiazhen, mai shekaru 60, ma'aikacin da ya yi ritaya daga lardin Henan: "In ka tsufa ba abin da ya rage maka sai rayuwarka. Ba abin da zai dame ka sai yanayin rayuwarka. Duk da haka ina ganin shugabanninmu sun damu da mu. Mu ma'aikata muhajirai muna jin dadi".
 • Zhao Panhui
  Zhao Panhui, mai shekara 65, mai wanke kwanuka a gidan abincin wata makaranta, daga Birnin Shijiazhuang, lardin Hebei: "Ina fata shugabannin China za su iya inganta rayuwar talakawa ta hanyar karin albashi mafi karanci. Suna kuma bukatar su tabbatar da tsaron talakawa".

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.