BBC navigation

Makarantu masu aiki da lantarkin hasken rana

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:56 GMT

Makarantu masu aiki da lantarkin hasken rana

 • Wani yaro ya hau makarantar kan ruwa
  Wani aikin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana a makarantun kan ruwa ya shiga jerin ayyukan da aka bayar da sunayensu don samun lambar yabo yayin Taron Ilimin Kirkire-kirkire a Makarantu, wanda za a yi a Doha, babban birnin kasar Qatar. Ayyukan da aka kebe sunayensu don a ba su lambar a bana ba kawai sauyi suka kawo a bangaren ilimi ba, sun kuma samar da wata dabara ta nemo kudi don tallafawa ilimin firamare.
 • Yara a cikin aji a wata makarantar kan ruwa
  Manufar aikin, wanda wata kungiya mai zaman kanta da ake kira Shidhulai Swanirvar Sanagstha ta kirkiro, ita ce samar da kayan aikin da za su tabbatar ba a samun tsaiko a makarantun Bangladesh, musamman a lokacin yanayi na damuna mai tsananin ruwa da iska.
 • Gidan wadansu mutane a gabar kogi
  Yawancin al'ummar yankin sun cunkusu ne a dan wani tudu da ke gabar kogunan da ke kai ruwa tekun Bengal sakamakon karancin filaye. Yankin da ke kusa da teku na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa; hakan kuma kan takaita zirga-zirga a yankin.
 • Wata yarinya tana aiki da kwamfiyuta
  Mohammed Rezwan, shugaban kungiyar Shidhulai Swanirvar Sangstha, dan asalin yankin gundumar Natore ne. A cewarsa, "Na dandana wahalar da mutanen bakin kogin ke sha, wadanda ba su da wata hanyar samun bayani da ire-iren damar da hakan ke kawowa. Ba dama dalibai su je makaranta idan ba hanya lokacin damuna mai tsanain ruwa da iska, wato monsoon.''
 • Wani aji a wata makarantar kan ruwa
  Rezwan ya samu samu horo ne a fannin zayyanar gine-gine, amma kuma ya rungumi wannan kaluble. "Abu ne gama-gari ka ga yaran da suka daina zuwa makaranta a wanann yankin, al'amarin da na kasa jurewa. Don haka na yi tunanin cewa idan yara ba za su iya zuwa makaranta ba saboda rashin abun hawa, to makarantar za ta zo musu har gida, ta kwale-kwale.''
 • Yara na shiga wata makarantar kan ruwa
  Kwale-kwalen da ke dauko yara daga kauyuka daban-daban na bakin kogin; kowanne kwale-kwale yana da wurin zaman 'yan aji guda da suka kai dalibai 30. Kwale-kwale 20 ne ke aiki kuma suna da jumlar dalibai 1,657.
 • Wani yaro yana duba littattafai a dakin karatun makarantar kan ruwa
  Baya ga kwamfiyutocin hannu da na tebur wadanda aka hada su da intanet, makarantar na da shiryayyen dakin karatu a cikinta.
 • Manya na daukar karatu a makarantar kan ruwa
  Makarantar tana bayar da ilimin firamare, sannan kuma tana da kwasa-kwasai da manya su ke yi a bangarori irin su aikin gona, da 'yancin mata, da kasuwanci da kuma dabarun fuskantar sauyin yanayi.
 • Wata yarinya tana karatu da fitilar a-ci-balbal mai amfani da hasken rana
  An kuma tanadi fitilar a-ci-balbal mai amfani da hasken rana, don dalibai su ci gaba da karatu a gida.
 • Yara na barin makarntar wata makarantar kan ruwa
  A yanzu haka ana samun kudin da ake amfani da shi don aikin ne daga masu bayar da tallafi na cikin gida da na kasashen waje, sai dai kungiyar tana kokarin nemo wata hanya ta daban ta samo kudade nan gaba. Hutuna: Shidhulai Swanivar Sangstha.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.