BBC navigation

Hotuna: Yarjejeniyar Isra’ila da Falasdinawa

An sabunta: 22 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:14 GMT

Hotuna: Yarjejeniyar Isra’ila da Falasdinawa

 • Hotuna: Yarjejeniyar Isra’ila da Falasdinawa
  Jama’a a birnin Gaza na yankin Falasdinawa sun fara yunkurin komawa harkokinsu na yau da kullum a ranar farko ta fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar da bangarorin biyu suka sanya hannu.
 • Hotuna: Yarjejeniyar Isra’ila da Falasdinawa
  Bayan shafe kwanaki takwas Isra’ila na lugudan wuta kan Gaza, birnin yayi kaca-kaca - filin wasan kwallon kafa na birnin na cikin wuraren da aka rusa.
 • Hotuna: Yarjejeniyar Isra’ila da Falasdinawa
  Hamas na ikirarin samun nasara kan yarjejeniyar zaman lafiyar – ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar hutu sannan ta shirya gagarumin taro wanda ya samu halartar shugaban kuniyar Isma’il Haniyeh.
 • Hotuna: Yarjejeniyar Isra’ila da Falasdinawa
  Anan, ‘yan sandan Hamas guda biyu sun rungume juna a gaban ginin hedkwatarsu da aka rusa a birnin Gaza.
 • Hotuna: Yarjejeniyar Isra’ila da Falasdinawa
  Sai dai ba duka ‘yan Gaza ne ke murnar yarjejeniyarba - wadannan iyalin da ke Khan Younis na zaman makokin dan uwansu ne da aka kashe sakamakon harin Isra’ila ranar Laraba.
 • Hotuna: Yarjejeniyar Isra’ila da Falasdinawa
  Wasu mazauna yankin da suka bar gidajensu sakamakon farmakin da Isra’ila ta yiwa lakabi da ‘Operation Pillar of Defence’, sun dawo sun taras da gidajen na su a rushe.
 • Hotuna: Yarjejeniyar Isra’ila da Falasdinawa
  Kasar Masar ce ta shiga tsakani – inda aka nemi Isra’ila da ta datakar da duk wani hari da take kaiwa ta sama, ta kasa ko ta ruwa, sannan ta dakatar da kai harin dauki dai-dai.
 • Wajibi ne Hamas da sauran kungiyoyi su daina harba rokoki zuwa Isra'ila da hari a kan iyaka. Za a fara tattaunawa kan yiwuwar bude kan iyakokin Gaza.
 • Hotuna: Yarjejeniyar Isra’ila da Falasdinawa
  Duka bangarorin biyu sun sha alwashin mayar da martani idan daya daga cikinsu ya sabawa yarjejeniyar – tankokin yakin Isra’ila sun ci gaba da kasancewa a kuwa da iyakar zirin Gaza.
 • Hotuna: Yarjejeniyar Isra’ila da Falasdinawa
  Wasu daga cikin ‘yan Isra’ila sun nuna fushinsu kan matakin gwamnatin kasar na shiga yarjejeniyar , ciki harda wadannan mutanen na garin Kiryat Malachi inda aka kashe Isra’ila wa uku sakamakon harin roka daga Falasdinawa a makon da ya gabata.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.