Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Ya ya ake shirin Kirsimatin bana?

Hoton Mujami'ar Milan
Image caption Hoton Mujami'ar Milan

Kirsimati dai buki ne da ake yi a duk shekara domin tunawa da haihuwar Annabi Isa (Alaihissalam ) ko kuma Yesu almasihu, wanda ake yi ranar 25 ga watan Disambar kowace shekara a ko'ina cikin duniya.

Ranar Talata mai zuwa ce mabiya addinin Kirista a ko'ina cikin duniya ke bukukuwan Kirsimeti. Shin a wane yanayi Kirsimetin ta bana ta riske ku, kuma wadanne abubuwa ne suka kamata a yi ,ko a kauce ma a lokacin bukukuwan?