Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda ake sace 'yan mata a India

Mutuwar wata daliba sakamakon fyaden da wasu gungun mutane suka yi mata a birnin Delhi na kasar India ya haifar da gagurumar muhawara kan makomar mata a tsakanin al'ummar kasar ta India.

Ana adana adadin matan da ake kashewa tun suna ciki da kuma jarirai. Sai dai abinda ba a sani sosai ba shi ne safarar 'yan mata a fadin kasar domin cike gurbin da ake da shi.

Wakiliyar BBC Natalia Antelava, ta gudanar da bincike ga kuma fassarar rahotonta:

Za ku iya sauraron cikakken rahoton na Natalia a shirin Turanci na gidan rediyon BBC wato Assignment...