Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Taƙaita sana'ar acaba

Wasu 'yan acaba
Image caption Miliyoyin matasa ne suka dogara da sana'ar acaba a Najeriya

Sana'ar acaba ko Okada kamar yadda ake kiranta a wasu jahohin Najeriya ta zama wata babbar hanyar dogaro da kai ga miliyoyin mutane a ƙasar.

Matsalar rashin aikin yi da ta zama ruwan dare gama duniya ta sa miliyoyin matasa rungumar sana'ar ta acaba, yayin da wasu kuma ke ganin ita ce mafi saukin zurga- zurga a cikin birane, don haka suka fi hawa acabar ko okada wajan gudanar da harkokinsu.

Sai dai kuma tun bayan da Najeriya ta fara fuskantar matsalar tsaro a 'yan shekarun nan, mahukunta a sassa daban daban na ƙasar suka fara ɗaukar matakai akan masu sana'ar acabar, suna masu zargin cewa ana amfani da su ne wajan kai hare- haren bama-bamai da kashe- kashen jama'a da ma satar mutane a wasu jahohi, kama daga kudanci zuwa arewacin ƙasar.

Jiha ta baya- bayan nan da ta dauki irin wannan mataki ita ce jahar Kano, inda ta ce ta hana goyo a babur, koda kuwa ba na haya ba ne, abin da wasu ke ganin wani mataki ne na hana sana'ar ta acaba a fakaice.