Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gidan kwalliya na farko a Ghana

Grace Amey Obenyg ta kawo sauyi a kasar Ghana, saboda ita ce 'yar kasar ta farko da ta bude gidan kwalliya a kasar haihuwarta.

Kuma a yanzu tana horar da dalibai dari biyar a kowace shekara.

Sai dai ta fuskanci kalubale a lokacin da ta fara kasuwancin, shekaru talatin da suka wuce musamman wajen samun jari.