Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Hira da Dan Masanin Kano

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

A Najeriya, batun kabilanci da bambancin addini da dai sauransu na ci gaba da zama wata gagarumar matsala, wadda ke yin barazana ga sha'anin zamantakewar jama'ar kasar.

Hakn kuma na barazana ga dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankalin mutanen kasar.

Hasali ma, ana ta bayyana fargabar cewa matsalolin sun yi kamarin da za su iya kaiwa ga wargajewar kasar.

Sai dai wasu dattawa kamar Dan Masanin Kano, Dokta Yusuf Maitama Sule na ganin irin wannan batu ba wani sabon abu ba ne a kasar, illa dai an sami tangarda wajen tafiyar da shugabancin kasar.

Amma kuma duk da haka, akwai kyakkyawan fatan cewa, za a iya shawo kan matsalolin, har al'amuran kasar su inganta.