Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Cutar Cancer ko ciwon daji

Wata yarinya mai fama da cutar cancer a Uganda
Image caption Cutar Cancer na kan gaba wajen hallaka jamaa a duniya

Cikin wannan makon ne dai aka yi bikin ranar yaƙi da Cancer, wato cutar daji a duk fadin duniya.

Taken ranar bana dai shi ne, kawar da duk wata gurguwar fahimta dangane da cutar ta daji.

Manufar dai ita ce, karawa jama'a fahimta dangane da cutar ta Cancer da kuma kawar da duk wasu tunani dake da nasaba da al'ada dangane da wannan cuta mai hallaka jama'a.

Hukumar lafiya ta duniya, wato WHO ta ce, cutar ta Cancer ce kan gaba wajen hallaka jama'a a duniya, kuma ta ce, koda a shekara ta 2008 cutar ta hallaka mutane fiye da miliyan bakwai.

A ƙasashen Afurka wannan cuta ta Daji na hallaka jama'a da dama saboda dalilai da dama da suka hada da rashin gano ta akan lokaci da kuma rashin kayan aiki a asibitoci domin kula da masu fama da cutar da kuma tunani iri iri masu nasaba da al'ada dangane da wannan cuta.