Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Hira da Mallam Nasiru El-Rufa'i

Tsohon ministan Abuja, babban birnin Najeriya, Mallam Nasiru El Rufa'i ya wallafa wani Littafi mai suna 'Accidental Public Servant' a Turance.

A littafin El-Rufa'i ya bayyana ayyukansa a karkashin tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo.

Mawallafin ya tabo wasu abubuwan da tsohon shugaban kasar ya yi, ciki har da yunkurin ta-zarce, abin da ya bayyana da cewa kura-kurai ne.

Kalaman da wasu 'yan kasar ke fassara su da cewa aibata Cif Olusegun Obasanjo ne.

A filinmu na gane-mani-hanya na wannan makon, Ibrahim Isa ya tattauna da Mallam Nasiru El Rufa'i a kan muhimman batutuwan da littafin ya kunsa.

Kuma ya fara ne da tambayarsa makasudin wallafa littafin.