Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sojoji na binciken gida-gida a Mali

Sojojin gwamnati a Mali na binciken gida-gida domin neman mayakan kungiyar Ansaruddin a garin Gao bayan harin ba-zaton da suka kai a garin ranar Lahadi.

Kwanaki kadan da suka gabata ne aka kore su daga garin - yayin da rahotanni ke cewa sojoji sun karbe iko da birnin, ga mazauna garin Gao zaman dar-dar ya sake karuwa.