Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Taba Kidi Taba Karatu: Hira da Adamu dan gambara a Najeriya

Kayan kida
Image caption Kayan kida

A wannan filin wakilinmu, Ishaq Khalid ya tattauna da dan gambara, mai suna Adamu dan gambara a jihar Bauchi dake Najeriya, wanda aka fi sani da na buta.

Gambara wata salon waka ce ta gargajiya a kasar Hausa, inda masu yinta wato 'yan gambara kan yi amfani da kalmomi ba tare da sakaye su ba, ko da kuwa kalmomi ne na batsa ko zambo.

Amma dai manufarsu ita ce ilmantar wa da fadakar wa da nishadantar wa.