Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Hira da Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso

Gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso
Image caption Gwamnatin jihar ta baiwa iyalan matan da suka mutu tallafin kudi tare da biyan kudin jinyan wadanada aka raunata a harin

Matsalar tsaro a Najeriya na cigaba da ciwa jama'a tuwo a kwarya a sassa daban-daban na kasar, musamman arewacin kasar.

Hakn na faruwa duk da matakan tsaron da gwamnatocin jahohin ke cewa suna dauka.

Inda ko a kwanakin baya wasu 'yan bindigan da ba'a san ko suwa nene ba, suka kai hari kan masu bada rigakafin shan inna ko polio, a jahar Kano dake arewacin kasar.

Harin da yayi sanadiyyar kashe akalla mutane tara dukkanninsu mata.

To ko wane mataki gwamnatin jahar ta Kano ta dauka bayan wannan hari da akai kai?