Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Dawowar sufurin jirgin kasa a Najeriya

A Najeriya, rashin kyawun hanyoyin na nufi sai an kwashe yini guda daga kudanci zuwa arewacin kasar idan za a yi tafiya a mota. Tafiya da mota da kuma jirgin sama sune hanyoyin da ake amfani da su kadai kafin a samu sauyi a kwananan. Sanya hannun jarin da kasar China ta yi a kasar ya sanya a yanzu haka an dawo da harkar sufurin jiragen kasa daga kudanci zuwa arewacin kasar wanda ake ganin zai hada kan al'ummar kasar. An dai bude sufurin jirgin kasa ne daga Lagos zuwa Kano.