Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Fargabar cin naman jaki a Kenya

A nahiyar Turai mutane na dari-dari game da naman da suke ci, saboda ana sayar musu da naman doki, a matsayin naman shanu.

Sai dai a gabashin Afirka kuwa labarin ya sha banban.

Domin a Kasar Kenya mutane ba su damu da naman doki ba, amma abin da ke daga musu hankalin shi ne naman jaki.