Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Zaben Kenya: Rana ba ta karya

Jama'ar kasar Kenya na kada kuri'a a zaben kasa baki daya a karon farko tun bayan zaben shekara ta 2007 wanda ya haifar da mummunan tashin hankali.

Wannan ne karon farko da ake gudanar da zabe a karkashin sabon tsarin mulkin kasar, wanda aka tsara domin kaucewa maimaita rikicin da ya biyo bayan zaben shekara ta 2007.

Sama da mutane 1,000 ne da ba basa ga maciji da juna suka rasa rayukansu, bayan rikicin da ya barke a wancan lokacin.

Duk da cewa dai an yi gangamin neman zaman lafiya, rahotanni sun ce an kashe jami'an 'yan sanda biyu a kusa da Mombasa da safiyar ranar Litinin.