Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan asalin Somalia mazauna Cardiff

Mutanen Somalia dake zaune a kasashen ketare, sun bazu cikin sassa daban-daban na duniya, kuma hakan ya faru ne biyo bayan tashin hankalin da kasarsu ta fuskanta a shekarun baya.

Sai dai a Birtaniya wasu 'yan Somalia sun samu matsuguni ne a gabar kudancin Wales tuna karni na 19.

A yau da dama daga cikin kakaninsu na zaune ne a garin Butetown dake makotaka da Cadiff, inda wani shirin hadin guiwa tsakanin cibiyar wasan kwaikwayo na Wales da kuma 'yan Somalia mazaun yankin ya fito, bayan kwashe shekaru an shirya shi.

Baya Cat ta halarci gurin domin gane wa idonta.