Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga:Shekaru biyu na mulkin Shugaba Isoufou

Image caption Shugaban Nijer, Alhaji Issoufou Mahamadou

A ranar 7 ga wannan watan ne, gwamnatin Jumhuriyar Nijar, karkashin jagorancin shugaba Alhaji Issoufou Mahamadou ta cika shekaru 2 a kan karagar mulki.

Gwamnatin dai ta ce ta samu nasarori da dama a tsawon wadannan shekaru 2 da suka hada da maido da martabar kasar a idon duniya tare da girka muhimman tsare tsaren bunkasa tattalin arziki da kyautata jin dadin rayuwar al'ummar kasar.

Sai dai kuma 'yan adawa karkahin kawancen ARN sun ce ikirarin da gwamnatin take yi, ba gaskiya ba ne, suna masu cewa har yanzu talakawa ba su gani a kasa ba domin har yanzu akwai fannoni da dama dake fuskantar matsaloli a kasar, kamar fannin ilimi da kiwon lafiya da kuma cin hanci da rashawa.