Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kade-kaden Afirka: Jaak mawakin rap

Ko ba komai, Jaak da gaske yake yi. Burinsa shi ne fadakar da al'ummarsa da ke Paal a Afirka ta Kudu marasa galihu, wadanda akan kira barbarar yanyawa.

Fatansa shi ne karfafa gwiwar matasa a tsakanin al'ummar tasa su yi alfahari ta tarihinsu. Wannan waka, 63,000, ta yi bayani ne a kan yadda aka kai kakannin kakanninsu bayi yankin da ake kira Cape, ta kuma suranta yadda rayuwarsu ta kasance da kuma yadda suke ji.

Jaak na matukar kaunar harshen Afrikaans, kuma yana cikin mutanen da ke taimakawa wajen karawa harshen armashi ta hanyar wakokin rap, da kuma wajen mallaka shi ga bakaken fatar da barbarar yanyawar Afirka ta Kudu wadanda shi ne harshen da suka gada.

Albom din Jaak na farko, Flêtse Maniere--ma'ana dabi'un unguwannin marasa galihu—a Afrikaans ta bayar da labarin yarintar Jaak shi da kansa. Ya rayu a unguwar marasa galihu, wato ghetto a Turance, inda ya yi ta fama da shaye-shaye—giya, da miyagun kwayoyi—da fadace-fadace, da fatara.