Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga:Barazana daga masu zafin kishin Islama

Image caption 'Yan Boko Haram a Najeriya

Kungiyoyin kishin Islama irin AQIM, wato kungiyar Al-Qaeda a yankin Magrib, da ta Ahlil Sunna Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram a Nijeriya, da al-Shabaab a Somalia, na daga cikin wasu kungiyoyin da a 'yan shekarun nan ke tayar da kayar baya a yankunan da suke.

Yankunan dake fuskantar irin wannan barazana a nahiyar ta Afrika sun hada da Kudancin Libya da Kudancin Aljeriya, da arewacin Nijar, da arewa maso gabashin Mauritaniya, da kuma galibin kasar Mali, da kuma a arewacin Nijeriya .

Saboda rashin kyakkyawan shugabanci ya sa yankunan masu fadi na hamada sun sa kungiyoyin na cin karen su ba tare da babbaka ba.

Hare hare na baya baya da ake dangantawa da irin wadannan kungiyoyi su ne wadanda aka kai a Agades da kuma Arlit a Nijar, inda aka kashe sojoji akalla 24.