Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Artabu tsakanin jami'an tsaro da 'yan Boko Haram

Image caption Jami'an tsaro a Maiduguri

Jami'an rundunar sojan Najeriya sun kammala ziyarar gani da ido na wuni biyu tare da manema labarai zuwa wasu sansanoni da hukumomin sojan ke ikirarin cewa na 'yan kungiyar Jama'atu Ahlul Sunna Lidda'awati Wal jihad ne, da aka fi sani da Boko Haram, kafin su fatattake su a arewacin jihar Borno.

Mustapha Muhammad na daga cikin tawagar 'yan jaridun da suka yi tafiyar, ya kuma hada mana rahoto na musamman, kan yadda tafiyar ta kasance, da halin da jama'a ke ciki