Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Hira da Firai ministan Nijar

Image caption Shugaban Nijar Muhammadou Issoufou

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce tana daukar duk matakan da suka dace domin hana sake aukuwar irin hare-haren ta'addancin da aka kaiwa kasar a watan Mayu.

Hare-haren dai sun auku ne a Agadez da Arlit da Yamai a watan Mayu da kuma farkon watan Yuni.

Kungiyar MUJAO dai wadda ta dauki alhakin hare-haren, ta kuma yi barazanar kai wasu karin hare-haren, idan har Nijar ba ta janye sojojinta daga kasar Mali ba.

Mutane fiye da mutane ashirin ne suka rasa rayukansu a hare-haren uku.

Yayin wata ziyara a London, inda ya halarci wani babban taro kan matsalar karancin abinci a duniya, Firai ministan Nijar, Malam Briji Rafini ya shaida wa Elhadji Diori Coulibaly cewa, yanzu gwamnatinsa na kara daura damara domin tunkarar irin wadannan mahara.

Firai ministan Nijar ya soma ne da yin bayani kan makasudin ziyarar tasa zuwa London;