Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Butun-butumin Japan zai tashi zuwa sararin sama

Wani Butum-butumin da japan ta kera domin ya yi aiki a sararin subahana, kuma ya yi magana baki da baki da 'yan sama jannati dake saman na shirin tashi zuwa tashar sama jannati ta kasa da kasa.

Wadanda suka kera butum-butumin na fatan, dan mitsitsin abin zai zama abin debe kewa ga dan sama jannatin kasar Japan Koici Wakata, a kokarinsa na isa tashar sama jannati ta kasa da kasa a watan Agusta.