Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Amsoshin Takardunku: Tarihin Edward Snowden

A wannan makon mun amsa tambayoyin da masu sauraro da dama suka aiko mana, na neman sanin tarihin ba Amurken nan tsohon jami'in leken asirin Amurka, Edward Snowden.

Haka kuma Dr. Habibu Sani Babura, Malami a sashen harsunan Najeriya a jami'ar Bayero ta Kano ya amsa tambayar hadin gwiwa da ta fito daga wasu masu sauraro, dake son su san ko me ake nufi da Allah ya fidda ga Rogo?