Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Hasashen ambaliya a Najeriya

A Najeriya hukumar kula da hasashen yanayi ta kasar ta ce, akwai yiwuwar a sake yin ambaliyar ruwa a wasu sassan kasar bana.

A bara dai mutane sama da miliyan biyu ne suka rasa matsugunan su, yayin da mutane sama da 300 kuma suka rasa rayukan su, haka kuma ambaliyar ta yi awon gaba da dabbobi tare da shafe gonaki.

Jihohin da ambaliyar ruwan ta shafa a shekarar data gabata sun hada da Adamawa da Plato da kuma Kogi.

Mustapha Muhammad ya ziyarci Jihar Kogi, a lokacin da babbar Jami'ar kula da bada agajin aggawa a karkashin ofishin Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Valerie amos ta kai ziyara Jihar.

Ya kuma hada mana rahoto na musamman kan fargabar da mutane ke ciki.