Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Taba Kidi Taba Karatu: Kyautar adabin Afrika ta Caine

A ranar Litinin 8 ga watan Yuli ne, a birnin Oxford na Birtaniya za a sanar da wanda ya yi nasarar lashe kyautar adabin Africa ta Caine ta shekarar 2013.

Wannan kyauta ce mai daraja da a kan ba wa marubuta gajeren labari, bisa la'akari da ci gaban da aka samu a al'adun tatsuniya na Afrika.

An dai zabi wasu marubata biyar ne daga nahiyar Africa, inda hudu daga cikinsu 'yan Najeriya ne da suka wallafa wasu gajerun labarai.