Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Masu tabin hankali a Najeriya

Wasu rukunin mutane wadanda ga alama kusan an manta da su a tsarin kiwon lafiyar Najeriya, su ne na masu tabin hankali duk da dimbin yawansu.

Wannan matsala bata tsaya kawai a Najeriyar ba, domin lamarin kusan hakan yake hatta a wasu kasashen dake nahiyar Afrika.

Rashin kulawa da rukunin wadannan mutane har ta sa da dama daga cikin mahaukata ko masu tabin hankalin kan yi gararamba a kan tituna.

Masu sharhi da dama na cewa barin mahaukatan su yi ta yawo cikin mummunan yanayi bai dace da kare hakkin bil-Adama ba, kuma hakan na kara cutar da su.

A filin mu na Gane Mini Hanya na wannan mako, mun duba abubuwan dake haddasa tabin hankali, da halin da masu tabin hankalin ke ciki a Najeriya da kuma matakan da ya kamata a dauka domin kyautata rayuwarsu.