Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Yaki da cutuka a Afrika

Image caption Sauro mai sa cutar Malaria

Kasashen nahiyar Afirka sun amince za su dauki dawainiyar yaki da cutar AIDS ko SIDA, da tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro a nahiyar.

Kasashen sun bayyana matsayinsu ne a wani kudirin da suka cimma a taron Kungiyar Tarayyar Afirka da suka kammala a Abuja.

A baya dai, nahiyar na samun sama da kashi tamanin bisa dari na kudaden da ake bukata don yakar wadannan cututtuka ne daga tallafin da manyan kasashen duniya ke ba ta.