Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Zaben Shugaban kasar Mali

Image caption Ana lika postan 'yan takara

Jibi idan Allah ya kaimu ake shirin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a Mali, a yunkurin sake kafa mulkin demokradiyya a kasar, bayan wani juyin mulki da kuma mamayar da Abzinawa 'yan-aware da masu kaifin kishin Islama suka yiwa arewacin Malin.

To shin yaya kuke kallon zaben ne? Kuma, ko zai haifar da zaman lafiya a Malin, da ma a yankin gaba daya?

A kan haka za mu tattauna, a filin Ra'ayi Rigar na yau.