Gane Mini Hanya: Hira da gwamna Rotimi Ameachi

29 Yuli 2013 An sabunta 11:54 GMT

Gwamnan jihar Rivers dake yankin Niger Delta mai arzikin mai a Najeriya, Rotimi Ameachi ya ziyarci ofishin BBC dake London.

Gwamnan ya kasance cikin wata takaddamar siyasa da ta shafi shugabancin kungiyar gwamnonin kasar da kuma ja-in-jan da ake fama da ita a majalisar jihar.

Shugaban sashen Hausa na BBC, Mansur Liman ya yi hira da shi game da batutuwan da suka shafi dambarwar siyasar.