Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya: Al'adar fulani ta Pulaako

Fulaaku wata halayya ce da ke tattare da matukar jin kunya ko kuma kara, wadda aka san Fulani da ita.

A sakamakon haka, a al'adance Bafulatani ba zai iya yin wasu abubuwa da sauran kabilu suka dauka ba wani abin kunya ko abin fada ba ne.

Sai dai kuma, sakamakon yadda zamanani ke ci gaba da kawo sauye-sauye a duniyar yau, su ma Fulani ana ganin sauyin irin na zamani a nasu tsarin rayuwar.

To, ko hakan ya shafi al'adar Fulanin nan ta Pulaaku?

Wakilinmu a Enugu, AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya bi sawun wannan batu.