Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bidiyon Fasaha

Image caption Hanyar sadarwa ta intanet

Wata kungiyar kamfanonin fasaha na wani yunkuri na samar da hanyar sadarwa ta Intanet ga mutane masu yawa a kasashe masu tasowa.

Facebook da Samsung da Ericsson da Nokia da Opera da Qualcomm da mediatech sun hada gwiwa domin yin wani shiri, wanda babu riba a cikinsa da suka sanya wa suna intanet.org.

Mark Zuckerberg na Facebook yace burin kamfanonin shi ne samar da intanet ga wadanda a yanzu basu da halin samunsa. Sun yi kiyasin cewa kashi daya cikin uku ne kawai na mutanen duniya ke samun intanet.

Satar Bayanai

A wannan makon ne kuma masu satar bayanai suka shiga shafin Facebook na Zuckerberg.

Da ma dai wani Bapalasdine marubucin manhajar kwamfuta, Khalil Shretah ya ba da rahoton rauni a matakan tsaron dandalin na Facebook, amma bayan jami'an da ke kula da tsaro na kamfanin sun gwale shi.

Shretah ya shiga shafin mahsahurin mai kudin, inda ya bar sako domin tabbatar da cewa lallai akwai wannan kafar.

Amazon

Amazon.com ya bi sahun wasu manyan shafukan intanet wadanda 'yan kwanaki tsakaninsu da juna suka fuskanci katsewar sadarwa a lokutan da aka fi ziyartarsu.

Shafukan Microsft outlook.com da New York Times ma sun fuskanci matsala, kamar dukkan shafukan Google har da na aika sakonni.

Wadanda suka yi nusan na 'yan mintuna, abin da ya janyo raguwar masu ziyara da kashi 40 cikin dari.

Kawo yanzu ba a kai ga gano dalilan da suka haddasa matsalar Amazon da Google ba.

PS4

Katafaren kamfanin lataroni na Sony ya sanar da ranar kaddamar da na'urar wasan kwamfuta na PS4 a wajen taron wasan kwamfuta da za a yi a Jamus.

'Yar karamar bakar na'urar, wacce za a iya wasa da ita a kuma kalli fina-finai za ta bayyana a kasuwannin Amurka da Canada a ranar 15 ga watan Nuwamba.

Sannan kuma za ta shiga kasuwannin Turai a ranar 29 ga watan na Nuwamba.

Abokin hamayyarsa Micrososft bai bayyana ranar da zai kaddamar da nasa sabon wasan na Xbox One ba.

Armadilo T

A karshe masu bincike a cibiyar binciken kimiyya da fasaha mai zurfi ta Koriya sun kirkiri wata mota da bata bukatar fili mai girma domin ajiye ta. Armadilo T, mota ce dake amfani da wutar lantarki, wadda da an taba wani madanni za ta kankance. Bayan nade ta mai tuka ta zai iya shigar da ita wurin ajiya ta hanayr amfani da wayar salula.