Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya: Jam'iyyar PDM

A Najeriya, Hukumar zaben kasar-INEC ta yi rajista wa wata sabuwar jam'iyyar siyasa mai suna PDM, wato Peoples Democratic Movement.

An dai yi wa jam'iyyar rajista ne a daidai lokacin da wasu jam'iyyun adawa ke ke dunkulewa wuri guda don kalubalantar jam'iyyar PDP mai mulkin kasar.

Wasu dai na zargin cewa jam'iyyar PDM din na da alaka da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar da wasu gwamnoni biyar na jihohin arewacin kasar da ke kuka da jagorancin jam'iyyar PDP.

Alhaji Bashir Yusuf Ibrahim shi ne shugaban sabuwar jam'iyyar PDM, kuma Ibrahim Isa ya tattauna da shi a kan makasudin kafa jam'iyyar da wadanda ke goya mata baya.