Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya: Tattaunawa da Nuhu Ribadu

Image caption Nuhu Ribadu, ya yiwa jam'iyyar ACN takarar shugaban kasa a 2011.

A 'yan shekarunan Najeriya na fuskantar matsalolin daban-daban musaman na karuwar tabarbarewar tsaro da cin hanci da rashawa.

Kawo yanzu dai wasu na ganin cewar hukumomi a kasar sun gaza wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Malam Nuhu Ribadu tsohon shugaban hukumar EFCC a Najeriya a makon da ya gabata ya bada ba'asi gaban wata kotu a London, a kan shari'ar da ake yi wa tsohon gwamnan jihar Delta, mai arzikin man fetur Mr James Ibori .

Daga bisani ya kawo mana ziyara a ofishinmu na London inda ya tattauna da Aliyu Abdullahi Tanko a kan batutuwa da dama hadda na jam'iyarsu ta adawa APC, amma dai Nuhu Ribadun ya soma ne da bayani a kan abinda ya wakana a kotun.