Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Taro a London kan zuba jari a Nigeria

An kammala taron kwanaki biyu a London na majalisar bada shawara kan yadda za a inganta tattalin arziki da kuma zuba jari daga 'yan kasuwa na kasashen waje a Nigeria.

Taron wanda ya samu halartar Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan da kuma wasu kusoshin gwamnati ana yinsa duk shekaru biyu-biyu ne domin ganin yadda kasar za ta samun bunkasar tattalin arziki.

Sai dai batun rashin lafiyar Shugaba Jonathan ne abinda ya fi jan hankali game da taron, saboda ya kasa halartar bukin bude taron kuma likitoci bayan sun yi masa gwaji suka bukace shi ya huta.

Aliyu Abdullahi Tanko ya halarci taron ga kuma ya rahoto na musamman da ya hada mana a filin Gane Mani Hanya.