Titin Nelson Mandela
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tunawa da Nelson Mandela

Ana alakanta baki dayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a Africa ta kudu, da kuma komawa turbar dimokuradiyya cikin ruwan sanyi a kan mutum daya tak, wato Nelson Mandela.

Tarihin wannan mutum ya sauya yanayin siyasar kasar, kuma al'amari ne da aka yi ta yabawa a fadin duniya ta hanyoyi daban- daban

A birnin Delhi na India, titin da aka yiwa lakabi da Titin Nelson Mandela, na dauke da wani kanti na saida alawa.