Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Shekaru 60 na sarautar Sarikin Ban Kano

A wannan makon ne ake bikin cikar sarkin Ban Kano, hakimin Danbatta Alhaji Mukhtar Adnan shekaru 60 yana rike da sarauta.

Sarkin Bai, wanda kuma ke daya daga cikin mutane hudu dake zabar sarkin Kano, a yanzu shi ne yafi kowa dadewa yana sarauta a fadar Kano.

Shi ne kadai ya rage a raye cikin mutane hudu da suka zabi Alhaji Ado Bayero, a matsayin sarkin Kano a shekarar 1963.

A cikin shirinmu na gane mini hanya na wannan makon, wakilin mu a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya tattauna da shi, inda ya fara da tambayar sa ko ya yake ji da ya kai wannan lokaci a kan kujerar hakimci?