Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 29/03/14

Kwanakin baya ne dai wasu gwamnonin Jihohin arewacin Najeriya suka je Amurka inda suka gana da wasu jami'an kasar ta Amurka da kuma na Norway da Denmark kan batutuwan da suka shafi sha'anin tsaro da ya addabi yankin na arewa musamman kuma arewa maso gabas.

Gwamna Aliyu Magatakarda Wamako na jihar Sokoto na daya daga cikin Gwamnonin, kuma a kan hanyarsa ta komawa gida ya yada zango a London, inda ya gabatar da wata mukala kan batun cikar Najeriya shekaru 100 da hadewar ta wuri guda a matsayin kasa daya.

Gwamna Wamakon ya ziyarji sashen Hausa na BBC inda suka tattauna da Aminu Abdulkadir kan batutuwa da yawa da suka shafi Najeriya.

A filinmu na Gane mani hanya na wannan mako, Aminu ya fara ne da neman jin ra'ayinsa kan taron kasa da ake yi yanzu haka a Najeriyar: