Gwamnatin Bauchi ta kwashe dalibai 255

Image caption Gwamna Isa Yuguda na Bauchi

Hukumomin ilimi a jihar Bauchi da ke arewacin Nigeria,sun kwashe illahirin dalibai mata su 255 dake rubuta jarabawarsu ta kammala sakandare a makarantar sakandaren 'yan-mata da ke garin Yana cikin karamar hukumar Shira.

An mayar da su ne birnin Bauchi, bayan wani hari da wasu 'yan-bindiga suka kai a makarantar a karshen mako.

Dama dai a lokacin harin, dalibai mata masu rubuta jarabawar karshen ne suka rage a makarantar saboda sauran daliban suna hutu.

Wannan matakin ya biyo bayan wasu mummunan hare-haren bama-bamai da bindiga ne da wasu suka kai a garin ciki hadda makarantar inda aka kona gidajen malamai.

Kwashe daliban ya zo ne yayin da ake ci gaba da zaman zullumi kan dalibai 'yan mata da 'yan Boko Haram suka sace a Chibok da ke jihar Borno.

Karin bayani