Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Birnin Aleppo ya zama fagen daga a Syria

A yayin da ake ci gaba da gwabza kazamin yaki a Aleppo, birni mafi girma Syria, rahotanni sun bayyana cewa dubban mutane ne aka kashe ko aka raunata ta ruwan bama-bamai da jiragen sama a wannan shekara.

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch, ta zargi dakarun gwamnatin Bashar Assad da yin ta'addanci a birnin, ta hanyar kai hare-haren kan mai uwa da wabi kan fararen hula ta sama, musamman ta yin amfani da wani katon bam da ake saka wa cikin ganguna da jirgi mai saukar ungulu ke jefo wa daga sama.

Tawagar BBC ta sami damar shiga Aleppo, damar ba kasafai ake samun irinta ba.

Wakilin BBC Ian Pannell da mai daukar hoto Darren Conway sun shafe kwanaki hudu a can, su kadai ne 'yan jaridun kasashen waje da suka ziyarci birnin tun a bara.