Amurka na takaicin satar 'yan Chibok

Kakakiin fadar White house Jay Carney Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Boko Haram ta fitar da bidiyo, inda Abubakar Shekau ya yi ikirarin sace 'yan matan

Amurka ta bayyana satar 'yan mata fiye da 200 a garin Chibok, a matsayin abin haushi da kuma takaici.

Kakakin fadar White house, Jay Carney , ya ce shugaba Obama na samun bayanai a kan yadda abubuwa ke wakana, kuma masu bashi shawara akan tsaro na sa ido akan lamari.

Ya ce ma'aikatar harkokin wajen Amurkar na magana da gwamnatin Najeriya, akan yadda zata taimakawa Najeriyar a kokarin da take yi wajen nema da kuma kubatar da 'yan matan.

Kawo yanzu ba'a san wurin da yan matan suke ba, kuma jama'a a na cigaba da nuna fushi akan gazawar gwamnati wajen gano inda 'yan matan suke.

Sai dai Mr. Carney ya ce Amurka na taimakawa masu bincike na Najeriya akan yadda zasu magance matsalar tayar da kayar baya.