Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima na adawa da tsawaita dokar
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shekara guda bayan sanya dokar ta-baci a Nigeria

A watan Mayun shekarar 2013 ne shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya sanya dokar ta baci a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa da ke arewa-maso gabashin kasar.

Hakan wani yunkuri ne na kawo karshen karin hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa.

Shugaba Jonathan ya ce karin tashe-tashen hankulan na bukatar "matakai masu tsauri".

Haka kuma an sanya dokar ne domin kare al'umma tare da basu tsaro.

Ga Habiba Adamu dauke da karin bayani.