Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shirye-shiryen zabe a kasar Malawi

Kusan kashi 40 ciki 100 na kasafin kudin Malawi ana samu ne ta hanyar tallafi daga kasashen waje amma kuma a yanzu dangantaka tsakanin kasar da wasu kasashen wajen ta soma tsami.

An dakatar da wasu tallafin kudi saboda batutuwan da suka shafi cin zarafin bil adama da kuma cin hanci da rashawa

A yayinda ake shirin gudanar da zabe a mako mai zuwa, Ibrahim Shehu Adamu ya duba mana irin mahawarar da ta dabaibaye harkokin siyasar kasar.