Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 31/05/14

A Najeriya yayinda ake cigaba da babban baron kasa a Abuja, wakilan sun yi mahawara a mako mai karewa kan wasu batutuwa da suka shafi harkokin addini.

Wasu daga cikin shawararin da wasu suka gabatar sun hada da gwamnati ta daina daukar nauyin gudanar da aikin Hajji da kuma ziyarar Ibadah a birnin Qudus.

Sai kuma batun sanyawa masallatai da kuma majamiā€™u haraji .

Wadannan batutuwa sun ja hankali. Yayinda wasu wakilan ke goyan bayan haka, wasu kuma sun soki matakin.

A kan haka ne Ibrahim Mijinyawa ya tattauna da malaman addinan biyu domin jin yadda suke kallon wadannan batutuwa, ga kuma yadda hirar ta su ta kasance: