Ba mu hana zanga-zanga ba - 'yan sanda

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rundunar 'yan sandan ta yi amai ta lashe

Rundunar 'yan sandan Nigeria ta ce ba ta ba da umarnin haramta taro ko zanga-zangar lumana a ko'ina cikin kasar ba.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce ta bayar da shawara ne kawai ga 'yan kasar da su dinga takatsantsan wajen gudanar da gangami musammam a birnin tarayya Abuja da kewaye, saboda barazanar tsaro.

Kungiyar #bringbackourgirls mai gangamin matsa wa gwamnatin Nijeriya lamba don kara azama wajen nemo 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace ta shigar da kara gaban kotu don kalubalantar umarnin haramta mata gangami a birnin Abuja.

Rundunar ta jaddada bukatar masu shirya irin wannan gangami su dinga neman shawara da jagorancin rundunar kafin gudanar da irin wannan taro don kauce wa faruwar duk wani abin ki

Karin bayani