Birnin salvador na daya daga cikin biranen da ake wasan cin kofin duniya a Brazil
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Salvador: Birnin Brazil mai alaka da Afrika

Brazil ce ruhin Afrika domin a nan ne nahiyoyi biyu suka hade a birni daya.

Sai dai a Fonte Nova, manyan taurarin 'yan wasa na gwabzawa a gasar cin kofin duniya.

Ada nan ne babban birnin kasar Brazil, kuma ta cikin birnin na Salvador ne aka shigar da mafi yawan bayi daga sassa daban daban na nahiyar Afrika.

Kuma al'adu irin na bayin da suka zo daga Afrika, sun ci gaba wanzuwa har zuwa wannan zamanin.