Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 12/07/14

Kashe-kashen da kungiyar Boko Haram keyi a Najeriya, ya jawo hankalin kasashen duniya, musanma bayan da kungiyar ta sace 'yan mata sama da dari biyu a garin Chibok, da ke Jihar Borno.

Tun bara ne aka fattaki 'yan kungiyar daga matattarar su watau Maiduguri.

Wani wakilin BBC yaje garin a asirce inda ya ga irin zaman dar-dar dinda mazauna Maidugurin ke ciki.

Saboda dalilan tsaro, ba, kuma zamu sakaye sunayen wadanda suka yi Magana dashi.