Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 19/07/14

A makon jiya ne aka gudanar da wani taron gabatar da mukala na zaman Farfesa Abdallah Uba Adamu na jami'ar Bayero shehun malami wato Farfesa karo na biyu.

Ya fara zama Farfesa ne a bangaren ilimi, yanzu kuma jami'ar ta Bayero ta ba shi Farfesa a bangaren hanyoyin sadarwa wato Mass Communication. Farsa Abdallah Uba Adamu dai ya shafe lokaci mai yawa yana gudanar da nazari kan fina finan Hausa, da kuma wakoki da mawakan na Hausa.

A yanzu dai shi ne mutum na farko da ya zama shehun malami wato farfesa karo na biyu a jami'ar ta Bayero, kuma daga cikin kalilan din malam jami'a a fadin Nigeria da suka samu irin wannan matsayi na nazari.

Sai dai a yanzu kuma ya ce ya dukufa domin zama farfesa karo na uku a wani bangaren kuma.

A filinmu na gane mani hanya na wannan makon, wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya tattauna da shi a kan ayyukansa na binciken, inda ya fara da tambayar sa yadda ya ji da aka nada shi Farfesa karo na biyu.